Ahlul Baiti



2.  Ra'ayoyin sashin musulmi sun tafi a kan cewar ya dace ga Allah (S.W.T.) Ya kallafawa bayi abin da yafi karfinsu, wannan kuwa sun fade shi ne domin dogara kan fahimta ta kuskure da suka yi wa wannan aya mai girma:

"Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)

Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Alkur'ani mai girma, cewa:

"Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286)

To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattauna-war Ahlulbaiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Alkur'ani.

Imam Sadik (a.s.) ya ce:

"Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su (ayyukan sabo). Kuma bai umarce su da abu ba face Ya sanya musu hanyar barin abin. Ba su zamowa masu riko (da umarnin) ko masu bari face da izinin Allah([180])".

Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa:

"Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta([181])".

An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba ya sake da bayinSa cikin mulkinSa. Shi ne Mamallakin abin da Ya mallakar masu, Mai iko kan abin da Ya ba su ikonSa. Idan bayinSa sun yi biyayya gare Shi, ba zai tare ko Ya hana su ba. Idan kuwa suka zabi su saba masa, in Ya ga damar tare su sai Ya yi, idan kuwa bai tare su ba suka aikata sabon, to ba kuwa Shi Ya jefa su ciki ba". Daga nan sai ya ce: "Wanda duk ya kiyaye wannan maganar, to lallai zai rinjayi mai sabawa da shi([182])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next