Ahlul Baiti



Alhafiz Imaduddin Abul Fida, Isma'il bn Umar bn Kathir yana cewa:

"Shi Abul Hasan, Ali al-Hadi, shi ne dan Muhammadal-Jawad dan Ali al-Ridha dan Musa al-Kazim dan Ja'afar al-Sadik dan Muhammad al-Bakir dan Ali Zainul Abidin dan Husain al-Shahid dan Ali dan Abi Dalib, daya daga Imamai goma sha biyu. Shi ne baban Hasan bn Ali al-Askari. Ya kasance mai yawan ibada mai zuhudu. Mutawakkil al-Abbasi ya mai da shi garin Samarra, inda ya zauna a can sama da shekaru ashirin da watanni, ya kuma yi shahada ne a can a shekara ta 254 bayan hijira([158])".

An ruwaito daga Yahya bn Harthama wanda Mutawakkil, sarkin Abbasiyawa, ya aika domin taho da Imam Hadi (a.s.) daga Madina zuwa Samarra, ya ce:

"Sai na tafi Madina, da na shiga garin sai mutanenta suka yi kuwwa mai tsanani wanda ba a taba jin irin ta ba, su na masu tsoron wani abu zai faru da Ali. Suna nuna wannan damuwa ce saboda ya kasance mai kyautata musu, mai lizimtar masallaci, ba ya wata karkata zuwa ga duniya. Sai na fara kwantar musu da hankali, ina rantse musu cewa ba a umurce ni da munana masa ba kuma na zo cutar da shi ba ne. Daga nan sai na binciki gidansa, ban sami kome bai sai Kur'ani da addu'oi da littattafan ilmi, a saboda haka sai na ga girmansa ya daukaka a idanuwana([159])".

11- Imam Hasan bn Aliyu al-Askari (a.s.):

Imam Hasan al-Askari kuwa shi ne dan Imam Ali al-Hadi (a.s.), shi ma tamkar mahaifansa masu kyautatawa yake wajen ilmi, masaniya, tsantsaini da jihadi. Malamai da ma'abuta tarihi sun ba da shaidar hakan. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu na masana, kamar haka:

Shamsuddin Abu Muzaffar, Yusuf bn Faragili, jikan bn Al-Jawziyya, yace: "Ya kasance malami mai gaskiya, ya ruwaito hadisi daga babansa da kakansa([160])".

1.  Ali bn Sabbag al-Maliki ya ce:

"Darajojin shugabanmu Abu Muhammad Hasan al-Askari suna nuni da cewa shi mai daraja ne dan mai daraja, babu wanda ke shakka ko kokwanton imaman-cinsa. Kuma na san cewa da ana sayar da karimci da waninsa ne mai saye shi kuwa mai sayarwa. Shi tilo ne a zamaninsa ba shi da na biyu, ba a kwatanta shi da kowa, ba shi da kishiya. Shi ne shugaban mutanen lokacinsa, shi ne kuma Imaminsu. Zantuttukansa daidaitattu ne, ayyukansa kuwa abin yabo([161])".

12- Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.):



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next