Akidojin Imamiyya



 

26- Biyayya Ga Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar ilminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa kamar yadda Taurarin suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W).

A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa ba sa rigonsa da magana kuma su da umarnninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.

 Mu mun mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne. kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu.

Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makale da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da’awowi da jayayya.

Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba.

Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya.

Kamar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu to nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran yin dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ce zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajibcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.

Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tabki”[34].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next