Akidojin Imamiyya



Ba ma imani ga Imamanmu (A.S) da abin da ‘Yan gullatu[35] da ‘Yan Hululiyya[36] suka yi ba, “Kalmar da take fita daga bakunansu ta girmama”. Surar Kahf 5.

Imaninmu game da su shi ne cewa su mutane ne kamar mu suna da abin da yake garemu kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah ya kebance su da karamarsa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance da karamarsa ya kuma ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita na da sifofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.

Da wannan ne suka cancanci su zamo Imaman kuma masu shiriyarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.

Imaminmu Ja’afar Assadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada kuyi musun sa ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.

 

29- Imamanci Sai Da Nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa ko harshen lmamin da ya aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da lmamin bayansa, hukuncin lmamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa da ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi ko kuma kaddamar da shi ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.

Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Talib Amiri (A.S) ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai’a a kan shugabancin Muminai Ranar Gadir Ya ce: ‘‘A saurara a ji duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi ka tozarta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya’’.

Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancin- -sa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina kuma halifana a bayana ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa dayawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne sai dai babu Annabi a bayana” Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar:

"Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u". Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u. Wannan dan littafin ba zai iya bin diddigin dukkan abin da ya zo na daga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi ko bayan- -insu ba game da wannan maudu’i[37].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next