Akidojin Imamiyya



 

22- Gaskiyar Addinin Musulunci

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin Musulunci za mu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Alkur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.

 Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan ke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da ke hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawa kamar Attaura da Injila da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.

Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.

Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gasgata da shi gasgatawa ne garesu kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba a kan musulmi ba ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota wadancan shari’o’i ba, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.

Na’am, idan da mutum, zai yi bincike game da Addinin Musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki daya.

Wato sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu ba mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabinda zai zo bayansa[31].

Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi

Amma musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya ba idan har mai da’awar ya yi da’awa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next