Akidojin Imamiyya



 

18- Annabawa Da Littattafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da ismarsu da tsarkinsu, musanta Annabcinsu kuwa da zaginsu da isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma gaskiyarsu.

Wadanda aka san sunayens da shari’o’insu kamar Annabi Adam (A.S) da Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Dawud (A.S) da Annabi Sulaiman (A.S) da Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da sauran Annabawan da Alkur’ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma Ya karyata Annabcin annabinmu a kebance.

Haka nan ya wajaba a yi Imani da littattafansu da abin da aka saukar musu. Amma Attaura da Injila da suke hannayen wadanda aka canzasu daga yadda suka sauka saboda abin da ya auku gare su na daga canje-canje da sauye-sauye, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S) saboda wasan da ma’abuta son rai da kwadayi suka yi da su, wadanda ake da su yanzu mafi yawancinsu ko ma dukkansu kagagge ne da ya aka farar a zamanin mabiyansu bayan wucewarsu (A.S).

 

19- Addinin Musulunci

Mun yi imani cewa kadai Addini a wajan Allah shi ne Musulunci, kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar Dan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da Dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar Musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za ta zo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin Musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.

Da an dabbaka Shari’ar Musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da dan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, da kuma zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.

Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa tun daga karni na farko kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Ba riko da Musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa Musulmi wannan mummunan cibaya ba sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar Musulunci da tozarta dokokinsa da yaduwar zalunci da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu da kebantattu da kuma baki dayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next