Akidojin Imamiyya



“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da ke ga kawukansu ”. Surar Anfak 53. Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa “Cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17. Da fadinsa Madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da Alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117. Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.

Ta yaya ake sauraron Addinin Musulunci ya tayar al’umma daga dogon barcinta alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Hakika imani da amana da gaskiya da ikhlasi tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa da makamantansu tun farkon assasa Addinin Musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa Aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halitta ce su ne nan gaba. Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta, wasunsu babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shudewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima da camfe-camfe da surkulle da wahamce-wahamce, da kuma yake-yake, da jayayya da alfahari, sai suka fada a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau Yammacin Turai wayayye fadakakke babban sanannen makiyin mlusulunci ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah Madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.

A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi[28]. Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gagagauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

 

20- Mai Shara’anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi kuma shi ne cikamakon Annabawa shugaban Manzanni kuma mafificinsu baki daya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamarsa a kyawawan dabi’u: “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin Alkiyama[29].

 

21- Alkur’ani Mai Girma

Mun yi imani cewa Alkur’ani wahayin Ubangiji ne kuma abin saukarwa daga Allah madaukaki a harshen AnnabinSa mai daraja, a cikinsa akwai bayanin komai da komai, shi ne mu’ujiza madawwamiya wadda ta gagari dan Adam ya zo da kamarta a balaga da fasaha da azanci tare da abin da ya kunsa na daga hakika da ilimomi madaukaka, jirkita ko canji ko karkacewa ba sa bujuro masa[30], Kur’anin da ke hannunmu wanda ake karantawa shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W), duk kuma wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, mai kawo rudu kuma mai rikitarwa kuma ba a kan shiriya yake ba, domin shi Kkur’an zancen Allah ne “Wanda Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa”. Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da suke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa duk sadda zamani ya cigaba, ilimomi suka da fannoni suka dada cigaba Kur’ani yana nan daram a kan danyantakarsa da zakinsa da daukakar manufofinsa da abin da ya kunsa na tunani, babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar yadda ba ya taba kunsar wani warwara game da hakika da yakini na falsafa, sabanin littattafan da malamai da manyan masanan falsafa komai matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani suka rubuta, sai ka samu wani abu na kuskure a cikinsu da tuntube. Kuma Kur’ani yana nan daram duk sa’adda aka samu cigaba a sababbin bincike na ilimi da sababbin ra’ayoyi. Kurakurai suna bayyana hatta a rubuce-rubucen manyan masala falsafar Yunan –Girika- kamar su Sakrato da­ Aplato da Arasto da duk wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma fifiku na tunani da amfani da kwakwalwa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next