Akidojin Imamiyya



Ya ce: To duk wanda ya so wanzuwarsu yana cikinsu, duk wanda ya kasance daga cikinsu shi mai shiga wuta ne.

Safwan ya ce: Sai na tafi na sayar da rakumana baki daya.

Idan son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu ya kai wannan matsayi, to ina ga wanda suke hada kai da shi a kan zalunci ko kuma yake karfafa su a zalunci, ina ga wanda ya shiga cikin jama’arsu ko yake aiki irin nasu ko yake bin tawagarsu ko kuma yake bin umarninsu?

 

40- Aiki A Hukuma Azzaluma

Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dibino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a “Tuhaful Uku1” daga Imam Sadik (AS)

Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. “Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al’amuran musulmi da su… wadannan su ne muminai na hakika. Su ne manarorin Allah a bayan kasa, su ne hasken Allah ne a cikin bayinsa…”. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja’afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma’aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz[49].

 

41- Hadin Kai A Musulunci

An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyu dan Abi Talib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko Musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki Musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next