Akidojin Imamiyya



 Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu’a da ta kunshi kyawawan dabi’u da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowanne ya sifantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo:

“Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da’a da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai da daidaita harsunanmu da daidaito da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha’inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa’aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da natsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al’umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta masu na daga hajji da umara don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahama”.

Kuma ni ina mai wasiyya ga ‘yan’uwana masu karatu da cewa kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S) Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai kuma ba ya kara wa mutum sani, ba ya sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki kuma ba a amsa masa addu’a da shi. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka sannan ka ji cewa lalle za a amsa”[39].

 

35- Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya

Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya suka yi dumu-dumu da jinin mutane sa’an nan suka yi watsi da koyar war Addini, sai Imam Zainul Abidin (AS) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusatarsa kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.

 Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur’ani da ladubban Musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS) kuma hanyar cusa wa mutane ruhin Addini da zuhudu da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u.

Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, a an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo da kuma ladubban Musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini da kyawawan dabi’u ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Alkur’ani da Littafin Nahjul Balagha.

Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah da kebewa da shi da sirrinka da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (S.A.W) da Manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunSa da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u.

Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da suke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau. Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin Musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next