Akidojin Imamiyya



Wannan akidar ta tashin kiyamar da saukin nan nata ita ce wacce Musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya wuce haka domin saninta dalla-dalla sama da abin da Kura’ani ya zo da ita domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike da masu kokwanto ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko bahasin dalili na zahiri to yana wahalar da kansa ne kuma zai fada a cikin mushkiloli da jayayya maras iyaka. A Addini babu adinda yake tilasta wannan zurfafawar dalla-dalla da littattafan masana Akida da malaman falsafa suke cike da shi, kuma babu wata larurar Addini ko ta zamantakewa ko siyasa da take tilasta irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da aka makale littattafai da ita babu wata fa’ida, wadanda suka karar da karfi da kokari da lokuta da tunanin masu jayaya ba tare da fa’ida ba.

Gamsuwarmu game da gazawar mutum game da riskar wadannan al’amuran da suke boyayyu a gare mu, kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu, sun wadatar wajen raddin wadannan shubuhohi da shakkun da ake tayarwa game da wadancan bayanai. Tare da sanin cewa Allah (S.W.T) mai iko ne a kan ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashi daga kabari. Ilimin dan Adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa mustahili ne su iya samo wani abu da bai san shi ba, ba ya kuma karkashin gwajinsa da bincikensa da ba zai iya saninsa ba sai bayan mutuwarsa da ciratarsa daga wannan duniya zuwa wata duniyar daban, idan haka ne yaya za a saurari ya yi huknci da tabbatarwa ko kore wannan abu balle ya shiga bayanansa dalla-dalla da abubuwan da suka kebanta da shi, sai dai idan ya dogara a kan bokanci da zato da mamaki kamar yadda yake a dabi’ar dan Adam ya yi mamakin dukkan abin da bai saba da shi ba, kuma iliminsa da riskarsa ba su san shi ba, kamar mai fada da jahilcinsa yana mai mamakin tashi daga kabari da tashin kiyama: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”.

Ba komai ne ya sa shi mamakin ba sai rashin sabawa da ganin matacce rididdigaggen an mayar masa da sabuwar rayuwa, sai dai mai wannan mamakin ya manta da yanda aka halicce shi tun farko alhalin da can ya kasance rasasshe, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu an hada su ne daga kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma sarari da abin ya tattaro har ya zama mutum madaidaici mai hankali: “Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsa”.

Ana gaya wa mai irin wannan maganar da ya mance kansa: “Wannan da ya fare ta tun karo na farko shi ne zai raya ta kuma shi masani ne game da dukan halitta”. Kuma a ce masa: Gashi bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abin da ya ba da labari game da shi, da gajiyawar iliminka hatta a gano sirrin halittarka da sirrin samuwarka, da yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin komai ba ya hankalta zuwa marhalolin da ke biye da aka harhada daga kwayoyin halitta manesanta, domin ka zamanto mutum madaidaici mai hankali mai tunani mai riska da mariskai. Kuma a ce da shi: Yaya kake mamakin dawo maka da rayuwa sabuwa bayan ka zama rididdigagge, kana kokarin tsinkayar sanin abin da kwarewarka ka da iliminka ba zasu iya gano shi ba?

A kuma ce masa: Ba ka da wata mafita sai mika wuya kana mai ikrari da wannan hakika wadda mai juya al’amuran halittu, masani, mai kudura, wanda ya samar da kai daga rashi. Kuma dukkan wani kokari na binciko abin da ba zai yiwu a gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne maras amfani, da rudani cikn dimuwa, da bude ido a cikin duhu mai dudum.

Dan Adam duk da irin inda ya kai gare shi na ilimi a wannan zamani, ya kago lantarki, da rada[58], da amfani da makamin kare dangi, da sauran kage-kagen da, da an yi magana game da su a shekarun baya da an kirga su a cikin mustahilan abubuwa ababan yi wa isgili, amma duk da haka mutum ya kasa gano hakikanin wutar lantarki, da sirrin kwayar zarra, ya kasa gano hatta hakikanin daya daga cikin siffofinta, to yaya zai ji kwadayin gano sirrin halitta da samuwa, sannan ya kara gaba yana son ya san sirrin Tashin kiyama da Tashi daga kabari.

Haka ne, ya kamata ga mutum bayan ya yi imani da Musulunci ya nisanci bin son zuciya kuma ya shagaltu da abin da zai gyara masa lahirarsa da duniyarsa, da kuma abin da zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abin da zai taimake shi a kansa da kuma abin da zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan halarta a gaban mai Mulki mai yawan sani. “Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta kuma ba a karbar fansa daga gareta kuma ba a taimakon su”. Bakara: 48.

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI

 

Karin Haske



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next