Akidojin Imamiyya



Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta haka ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari. Idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Alkur’ani ya ba da Iabari game da shi to sun yi hannun riga da Musulunci.

Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhali yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi.

Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu ba ne game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa ba don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S) wanda yake mai shiryarwa, wanda aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi.

 

32- Raja’a (Komowa Duniya)

Abin da Mazhabar Ja’afariyya Imamiyya ta tafi a kansa da riko da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) Shi ne cewa Allah (S.W.T) zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma sakawa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).

Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashi, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Alkur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu to mun yi furuci da zunubanmu shin akwai wata hanyar fita”. Surar Mumin: 11.

Na’am Alkur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, kuma mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa ma’anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S) da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko raya matattu.

Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya kuma aibi gare shi wanda yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da shi da aibata su da shi.

Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsayin zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai halatta wannan ba domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko da Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa. Kuma ita tamkar mu’ujizar raya matattu ce wacca ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su karon farko shi ne zai raya su kuma shi game da dukkan halittu masani ne”. Surar Yasin: 79-87.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next