Akidojin Imamiyya



Sannan ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah da tadabburi a cikin addu’a ta 6: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta dare da rana da karfinSa, ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa, ya sanya wa kowanne daga cikinsu iyaka ayyananniya, yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan’uwansa, da kaddarawarsa ga bayi a cikin abin da yake ciyar da su kuma yake sanya su su girma. Sai ya halitta musu dare domin su huta daga wahalar kaiwa da komowa da dawainiya, kuma ya sanya shi sutura domin su lulluba da hutunsa sai ya zama musu wartsakewa da karfi domin su sami jin dadi da sha’awa da shi. Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa’idar halittar rana da dare da kuma abin da ya kamata mutum ya yi godiyarsa na daga wadannan ni’imomi.

A wani salon kuma na bayanin dukkan al’amura ga Allah (S.W.T) suke za ka karanta a addu’a ta 7 cewa: “Ya wanda da Shi ne ake warware kulle-kulle! Ya wanda da shi ne kaifin tsanani yake dakushewa! Ya wanda daga gare Shi ake neman mafita zuwa yalwar sauki! mawuyatan al’amura na rusunawa ga kudurarka! sabubba suna tasiri ne da ludufinka kaddarawarka kuma ta gudana ne a bisa ikonka, abubuwa suna zartuwa da iradarka ne, suna masu umartuwa da iradarka ba tare da fadarka ba, kuma masu tsawatuwa ne da nufinka ba tare da haninka ba.

Na Biyu: Bayani game da falalar Ubangiji ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Ubangiji komai abin da ya yi na da’a da ibada kuwa, da kuma yankewa domin komawa zuwa ga Ubangiji kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 37: “Ya Allah hakika babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka sai wata Kyautatawarka ta same shi waccea za ta sake lizimta masa wata godiyar, kuma ba ya kaiwa ga matukar da’arka koda kuwa ya dage sai ya gaza yin yadda ka cancanta ga falalarka, Mafificin mai godiya gare ka a bayinka ya gaza a kan godiyarka, kuma mafi bautarsu mai takaitawa ne ga bautarKa”.

Saboda girman ni’imomin Allah (S.W.T) kan bawansa da ba su da iyaka bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi, yaya kenan idan kuma ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abin da fakara mai zuwa ta addu’a ta 16 take nunawa: “Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta fadi, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage kuma in yi ruku’u gareka har bayana ya sance, kuma na yi maka sujada har kwayar idandunana su faffado, kuma turbayar kasa ta cinye duk tsawon rayuwata, kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen rayuwata, sa’an nan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sannan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga munanan ayyukana ba.”

Na uku: Sanar da lada da ukuba da aljanna da wuta da kuma cewa ladan Ubangiji dukkaninsa kyauta ne kawai kuma bawa yana cancantar azaba ne da mafi karancin sabo da ya yi, kuma Ubangiji yana da hujja a kansa game da haka.

Kuma dukkan addu’o’in Sahifatus Sajjaddiya sun kawo maganar irin wannan azaba mai mai tasiri domin tsoratarwa da sanya tsoro a zuciya da sanya mata sa tsammani da ladan Ubangiji, dukkan wannan shaida ce a kan haka ta salo daban- daban da yake sa wa zuciya tsoron kan sabo. Kamar abin da zaka karanta a addu’a ta 46:- “Hujjarka tabbatacciya, Shugabancinka tsayayye ne ba ya gushewa, don haka tsananin azaba Madawwamiya ta tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gare ka, tsiyacewar tsiyata ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, kaikawonsa a cikin ukubarka ya tsawaita, bukatarsa ga burinsa na samun sauki ya nisanta, saukin samun mafitarsa abin yanke kauna ne, adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, da kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, hakika ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzurori…”

Kuma kamar yadda kake karanta addu’a ta 31: “Ya Allah! ka ji kan kadaitakata ta gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka, da firgicewar gabobina don haibarka, kuma ya Ubangijina! zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a farfajiyarka, idan na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba.”.

Kamar kuma karantawarka a addu’a ta 39: “Domin kai idan har ka saka mini da gaskiya to za ka halakar da ni, idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to za ka halakar da ni, kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda daukar nauyinsa ya gajiyar da ni, ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyarsa, kuma ka ba wa raina kanta saboda zaluncinta…”.

Na Hudu: Jan mai addu’a zuwa ga dauke sawunsa daga aikata munanan ayyuka da kaskantantun siffofi domin wanke ruhinsa da tsarikake zuciyarsa, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 20: “Ya Allah ka cika mini niyyata da ludufinka, kuma ka inganta mini yakinina da abin da ke gare ka, ka gyara min abin da ya baci daga gare ni da kudurarka, Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad ka jiyar da ni dadi daga shiriya ingantacciya da ba zan taba neman musanya daga gareta ba, da kuma hanya ta gaskiya wacce ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ba zan taba kokwanto a cikinta ba.

Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi ne da ake aibata ni da shi sai ka gyara shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi sai ka kyautata shi, ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shi”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next