Akidojin Imamiyya



Na biyar: Sanya wa mai karanta addu’ar dauke sawunsa daga mutane da rashin kaskantar da kansa gunsu, kuma kada ya kai kukan bukatarsa gun wani ba Allah ba, domin kwadayin abin da yake hannun mutune yana daga cikin mafi munin abin da mutum zai siffantu da shi kamar yadda zaka karanta a addu’a ta 20: “Kuma kada ka fitine ni da neman taimakon waninka idan na matsu da kuma kaskan da kai don tambayar wani ba kai ba idan na bukata, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, saboda haka sai in cancanci tabarwarka da haninka da kawar da kanka”.

Da kuma misalin addu’a ta 28: “Ya Allah ni na tsarkake niyyata da yankewa zuwa gare, kuma na juyo zuwa gare ka baki daya, kuma na kawar da fuskata daga dukan wanda bai wadata da falalarka ba, na ga cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wauta ce kuma bacewar hankalinsa ne.”

Da kuma misalin abin da kake karantawa a addu’a ta 13: “Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka kuma ya yi kokarin kawar da talauci da taimakonka, hakika ya nemi bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta fuskarta da ta dace. Wanda kuma ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma ya sanya shi sababin samunta ba kai ba, to hakika ya jawo wa kansa hani kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare ka”.

Na Shida: Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka wa sashensu ga sashe, da fifita juna a tsakaninsu domin tabbatar da ma’anar yan’uwantakar Musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 38: “Ya Allah! ni ina mai neman uzuri daga gare ka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da kuma wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba, da kuma duk wani mummunan aiki da aka nemi uzurina ban bayar da uzuri ba, da kuma duk wani mabukaci da ya roke ni ban ba shi ba, da kuma hakkin mai hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika masa ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba…”.

Hakika irin wannan neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abin da zai fadakar da zuciya zuwa ga abin da aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi’u madaukaka.

 A addu’a ta 39 akwai karin haske a kan hakan, sai ya sanar da kai yadda za ka yafe wa wanda ya munana maka, yana kuma gargadinka game da yin ramuwar gayya, yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakku: “Ya Allah duk wani bawa da ya yi mini abin da na hana shi a kansa, ya kuma keta mini abin da na kange shi gareshi, sai mutum da nauyin zaluntata, ko zuciyata ta tuna shi yana rayayye, to ka gafarta masa abin da ya yi mini ka yafe masa abin da ya riga ya gabatar gareni, kada ka tsayar da shi don tambaya a kan abin da ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abin da ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su da kama kyautar da na yi musu na daga sadaka gare su ya zama mafi tsarkin sadakar masu sadaka, kuma mafi daukakar addu’a ma’abota kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da addu’ata gare su rahamarka, har ya kowanne daga cikinmu ya rabauta da falalarka”.

Mamaki ya girmama ga wannan fakarar ta karshe! da kuma yawan girman tasirinta a cikin zukatan masu alheri! Domin dadakar da ita a kan kyakkyawar nufi ga dukkan mutane da nema wa kowa sa’ada hatta wanda ya zalunce shi. Irin wannan yana da yawa a cikin addu’o’in Sahifatus sajjadiyya, da yawa daga irin wadannan koyarwa ta ubangiji ga tsarkake rayukan ‘yan Adam da sun kasance masu shiryuwa.

 

36- Ziyartar Kaburbura

Ziyarar kaburbura -Annabi da na Imamai (AS)- da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abu mai tsada da mai sauki a cikin imani da dadin rai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next