Akidojin Imamiyya



Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirin samuwarsa da karamarsa, da wato ba zai sami wani ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuma yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (A.S) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta domin kada wahami ya yi galaba a kansa sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa.

Mafi isa matuka daga wannan a suranta haramcin taimakekeniya da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (AS) wanda ya kasance daga cikin shi’ar Imam din, kuma daga masu rawaito hadisinsa amintattu (kamar yaddda ya zo a littafin Rijal na Alkashi game da Safwan) ya ce: “Na shiga wajansa.

Sai ya ce da ni: Ya Safwan duk wani abu daga gareka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu daya.

Na ce: A sanya ni fansa gare ka! Wane abu ne?

Ya ce: Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.

Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai ashararanci, ko dagawa, ko don farauta, ko wasa ba, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato hanyar Makka kuma ba na aikin da kaina sai dai ina tura shi da bayina.

Ya ce: Ya Safwan kudin hayarka yana zama bashi a kansu?

Na ce: Na’am, a sanya ni fansa gare ka.

Ya ce: Shin kana so su wanzu har su biya ka kudin hayarka?

Na ce: Na’am.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next