Akidojin Imamiyya



Kamar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu to nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran yin dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ce zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajibcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.

Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tabki”[34].

Ka zurfafa tunaninka game da wannan hadisi mai girma zaka samu abin da zai gamsar da kai ya kuma girgiza ka a wannan hadisin a ma’anarsa a fadinSa (S.A.W): “Matukar kun yi riko da shi ba ku taba bata ba a bayana har abada” abin da ya bar mana su ne sakalaini tare ya kuma sanya su abubuwa guda biyu, bai iso da riko da daya ba, ba tare da dayan ba, da riko da su ne ba zamu taba ba har abada. Duba kuma ma’anar fadinsa (S.A.W) cewa: “Ba zasu taba rabuwa ba har sai riske ni a tabki” da nunin cewa wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su a hade ba to ba zai taba samun shiriya ba har abada, don haka ne suka zama su ne; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba gudu ne daga gaskiya da ba abin da ke kaiwa ga hakan sai bakin ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici a fassarar bayanan zancen Larabci mai fasaha.

 

27- Son Ahlul Baiti (A.S)

Madaukakin sarki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S) wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da ta manzansa wanda kuma ya ki su to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).

Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasiba” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyara Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin Musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon Musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin funafunci son su kuma ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da Manzonsa,

Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da Manzonsa da tsarkinsu da nisantar su ga shirka da sabo da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba kuwa to da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.

 

28- Matsayin Imamai (A.S)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next