Akidojin Imamiyya



Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zato”. Surar An’am: 116

A hakika mu abin da muke yin imani da shi shi ne cewa: Hankulanmu su ne suke wajabta mana yin tuntuntuni kan halittu da sanin mahallicin duniya, kamar yadda suke wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar annabta da kuma mu’uijzarsa. Kuma bai inganta ba -a hankalce- a yi koyi da wani a cikin wadannan al’amuran komai matsayinsa da darajarsa.

Abin da ya zo a cikin Alkur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali da ra’ayoyin ma’abota hankali suka ginu akansu, ya kuma zo ne don fadakar da mutane abin da aka halitta su a kansa na sani da hankaltuwa da tunani da kuma bude –fadada- tunani da fuskantarwa zuwa ga abin da hankula suke hukunci da shi.

Ba daidai ba ne -a irin wannan hali- mutum ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane masu tarbiyyantarwa kan wata akida ko wasu mutanen daban. A’a ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa[4] wadanda ake kira shika-shikan Addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi -Kadaita Allah-, da Annabci, da Imamanci, da kuma Tashin kiyama.

Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada.

 A takaice dai mu muna da’awar abubuwa biyu ne:

Na Farko: Wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba.

Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari’a, wato saninsa bai samo asali daga nassosin Addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi.

Kuma ba komai ake nufi da ma’anar wajabcin hankali ba sai riskar hankali ga larurar sani da kuma lizimtar yin tunani da kokarin bincike a cikin shika-shikan Addini.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next