Akidojin Imamiyya



6- In kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.

7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana’izarsa. Idan kuma ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ita, sai dai ka gaggauta masa.

Sannan ya rufe maganarsa da cewa: “Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa kuma soyayyarsa da soyayyarka”.

Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma’anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S) wasunsu daga littafin Wasa’il a babobi daban-daban.

Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da ‘yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu’awiya Dan Wahab ya ce[53]:

Na ce masa[54]: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al’amarinmu”.

Sai Ya ce: “Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu suna halartar jana’izarsu suna ba da shaida gare su da kuma da kansu kuma suna bayar da amana gare su.”

Amma ‘yan’uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci, kuma kai ka riga ka ji wasu hadisai a fasalin bayanin sanin shi’a da ya gabata. Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin[55] da Abbana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.

Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?

Na ce: Na’am.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next