Akidojin Imamiyya



2- Koyi Da Wani A Rassan Addini

Amma rassan al’amuran Addini su ne hukunce-hukuncen shari’a wadanda suka shafi ayyuka, su bai wajaba ba a yi nazari da ijtihadi a kansu ba, wajibi ne a cikin rassan hukunce-hukucen addini idan ba laruran Addini ne ba ne kamar wajabcin salla, da zakka, da azumi, da hajji, mukallafi ya yi dayan al’amura uku a cikinsu:-

Ko ya yi ijtihadi[5] ya yi bincike a kan dalilan hukunce-hukunce idan yana cikin masu iya yin hakan, ko kuma ya zama mai ihtiyadi idan zai iya yin ihtiyadi[6], Ko kuma ya yi koyi da Mujtahidin da ya cika sharruda. Ya kasance wanda zai yi takalidi da shi mai hankali ne, Adali, mai kare kansa, mai kiyaye Addininsa, mai saba wa son ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa.

Duk wanda ba Mujtahidi ba ne, kuma ba mai yin ihtiyadi ba, kuma bai yi koyi da mujtahidin da ya cika sharudda ba, to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla, ya yi azumi, ya yi ibada duk tsayin rayuwarsa, sai dai idan aikinsa ya dace da ra’ayin wanda yake yi wa takalidi kuma ya yi sa’ar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah (S.W.T).

 

3- Bayanin Ijtihadi

Mun yi Imanin cewa: ljtihadi a rassan hukunce-hukuncen shari’a wajibi ne kifa’i[7] da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam, wato ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Sai dai idan wadanda suka wadatar sun dauki nauyin yi, to ya saraya daga kan sauran musulmai, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya cika sharuddan, sai su yi masa takalidi, su koma masa a cikin al’amuran hukunce-hukuncen Addininsu.

A kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami wanda ya sadaukar da kansa a tsakaninsu ya kai ga matsayin Ijtihadi wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo, kuma ya kasance ya cika sharuddan da ya cancanci a yi masa takalidi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen Addininsu. Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to ya wajaba a kan kowane daya daga cikinsu ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya wanda zai dukufa domin kai wa ga wannan matsayi a tsakaninsu, tunda ba zai yiwu ba dukkansu su dukufa domin neman wannan al’amari ko kuma zai yi wahala, Kuma bai halatta ba su yi takalidi da wanda ya mutu na daga cikin Mujtahidai.

Ijtihadi: Shi ne nazarin dalilan shari’a domin samun sanin hukunce-hukuncen shari’ar da shugaban Manzanni (S.A.W.) Ya zo da ita kuma ba ta sakewa ko canzawa da canzawar zamani da kuma halaye.

 â€œHalal din Muhammad (S.A.W) halal ne har zuwa ranar Tashin Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa Ranar Tashin Kiyama.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next