Akidojin Imamiyya



“Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarka”. Yi tunani a kan wannan kalma, “Ka rufe ni” a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka, a kan wannan al’amari ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan bayan waccan:

“Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubin”. Wannan irin ikrari daga cikin zuciya da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (S.W.T) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu’ar asiri da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah ya yi godiya gare shi, da ya yi masa afuwa baicin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa:

“Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka da yafewarka bayan kudurarka”. Sa’annan kuma addu’ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (S.W.T) domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa yayin da yake cewa:

 â€œKuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka kuma Suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta”.

Wannan shi ne tsarin salon addu’ar a ganawa ta asirce ta tsakake zukata, da saba musu da da’a da barin aikata sabo. Wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka ga su yawan gaske.

 Salon kafa tattauna da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni kamar yadda ya zo a Addu’ar Kumail Bn Ziyad:

“Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, sannan kuma yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba.”

Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sa’annan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa, ta wani bangare a boye domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa ya aikata idan har bai aikata shi ba.

Karanta wani salon addu’ar da a ke neman uzuri a cikin ita wannan addu’ar da cewa: “Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!”.

Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (S.W.T) da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa ne don soyayya da bege gare shi da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya yi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu’ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah yadda zai yafe ya yi masa rangwame. Mamaki da kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubi na taushin wannan salo ba zai buya ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next