Akidojin Imamiyya



Kuma mun yi imani da wajabcin girmama Kur’ani mai girma da daukaka shi a cikin magana ko a aiki, bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda ake dauka cewa ita yanki ce daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take, Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ba ya taba kalmominsa ko harrufansa: “Babu mai shafarsa sai wadanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79. Sawa’un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne, sai dai idan sun yi wanka ko alwala kamar yadda bayani dalla-dalla ya zo a cikin littattafan fikihu.

Haka nan bai halatta ba a kona shi ko wulakanta shi ta wace fuska da abin da yake wulakanci ne a ganin mutane, kamar jefar da shi ko sanya masa kazanta, ko shurinsa da kafa, ko sanya shi a wuri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi yana daga cikin masu karyata Addinin Musulunci da alamominsa masu tsarki, kuma shi abin hukuntawa ne da fita daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.

 

22- Gaskiyar Addinin Musulunci

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin Musulunci za mu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Alkur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.

 Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan ke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da ke hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawa kamar Attaura da Injila da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.

Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.

Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gasgata da shi gasgatawa ne garesu kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba a kan musulmi ba ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota wadancan shari’o’i ba, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.

Na’am, idan da mutum, zai yi bincike game da Addinin Musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki daya.

Wato sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu ba mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabinda zai zo bayansa[31].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next