Akidojin Imamiyya



A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi[28]. Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gagagauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

 

20- Mai Shara’anta Musulunci

Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi kuma shi ne cikamakon Annabawa shugaban Manzanni kuma mafificinsu baki daya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamarsa a kyawawan dabi’u: “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin Alkiyama[29].

 

21- Alkur’ani Mai Girma

Mun yi imani cewa Alkur’ani wahayin Ubangiji ne kuma abin saukarwa daga Allah madaukaki a harshen AnnabinSa mai daraja, a cikinsa akwai bayanin komai da komai, shi ne mu’ujiza madawwamiya wadda ta gagari dan Adam ya zo da kamarta a balaga da fasaha da azanci tare da abin da ya kunsa na daga hakika da ilimomi madaukaka, jirkita ko canji ko karkacewa ba sa bujuro masa[30], Kur’anin da ke hannunmu wanda ake karantawa shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W), duk kuma wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, mai kawo rudu kuma mai rikitarwa kuma ba a kan shiriya yake ba, domin shi Kkur’an zancen Allah ne “Wanda Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa”. Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da suke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa duk sadda zamani ya cigaba, ilimomi suka da fannoni suka dada cigaba Kur’ani yana nan daram a kan danyantakarsa da zakinsa da daukakar manufofinsa da abin da ya kunsa na tunani, babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar yadda ba ya taba kunsar wani warwara game da hakika da yakini na falsafa, sabanin littattafan da malamai da manyan masanan falsafa komai matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani suka rubuta, sai ka samu wani abu na kuskure a cikinsu da tuntube. Kuma Kur’ani yana nan daram duk sa’adda aka samu cigaba a sababbin bincike na ilimi da sababbin ra’ayoyi. Kurakurai suna bayyana hatta a rubuce-rubucen manyan masala falsafar Yunan –Girika- kamar su Sakrato da­ Aplato da Arasto da duk wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma fifiku na tunani da amfani da kwakwalwa.

Kuma mun yi imani da wajabcin girmama Kur’ani mai girma da daukaka shi a cikin magana ko a aiki, bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda ake dauka cewa ita yanki ce daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take, Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ba ya taba kalmominsa ko harrufansa: “Babu mai shafarsa sai wadanda suke tsarkakakku”. Surar Waki’a: 79. Sawa’un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne, sai dai idan sun yi wanka ko alwala kamar yadda bayani dalla-dalla ya zo a cikin littattafan fikihu.

Haka nan bai halatta ba a kona shi ko wulakanta shi ta wace fuska da abin da yake wulakanci ne a ganin mutane, kamar jefar da shi ko sanya masa kazanta, ko shurinsa da kafa, ko sanya shi a wuri wulakantacce, Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi yana daga cikin masu karyata Addinin Musulunci da alamominsa masu tsarki, kuma shi abin hukuntawa ne da fita daga Addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next