Akidojin Imamiyya



Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamar sa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Talib (AS) kamar fadinsa shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga a Nahjul balagha huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.

Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.

Na’am, hakika zalunci yana daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta saboda haka ne zarginsa ya zama abu ne farko da ya zo a hadisan Ahlul Baiti (A.S) da addu’o’insu da kuma nesantar da mabiyansu daga gare shi.

Wannan ita ce siyasarsu (AS) kuma a kanta suke mu’amala hatta da wanda yake yi musu shisshigi yake rashin kunyar hawa matsayinsu. Kissar imam Hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuma ya tausaya masa ya kuma tausasa masa har sai da shi ya ji kunyar mummunan abin da ya aikata. Kuma ka riga ka karanta abin da ya gabata a addu’ar shugaban masu sujjada na daga ladubba madaukaka game da afuwa ga masu ketare iyaka da nema nema musu gafara. Wannan kuma shi ne matukar abin da daukakar ran mutum da kamalar mutumtakarsa, duk da kuwa ketare haddin azzalumi kwatankwacin yadda ya ketara ya halatta a shari’a, kamar yadda yin addu’a a kansa ya halatta, sai dai halatta wani abu ne, afuwa kuma wacce take daga kyawawan dabi’u wata aba ce daban, kai gun imamai shige gona da iri wajan yin addu’a a kan azzalumi ana kirga shi zalunci.

Imam Sadik (A.S) ya ce: “Bawa yana kasancewa abin zalunta, ba zai gushe ba yana ta yin addu’a har sai ya zamanto azzalumin”. Idan wannan shi ne halin wanda aka zalunta to yaya halin wanda ya fara zalunci da ketare iyakar tun karon farko! Yake kuma cin mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu, yana munafuncinsu gun azzalumai, ko yake yaudarar su, yana ya jefa su cikin halaka, ko ya cutar da su ko ya yi leken asiri a kansu? Irin wadannan a wajan Ahlul Baiti (AS) su ne mafi nesantar mutane a wajan Allah, mafi tasananinsu sabo da azaba, mafi muninsu ayyuka da dabi’u.

 

39- Taimakekeniya Da Azzalumai

Yana daga –abin da yake nuna- yake nuna girman zalunci da mummunan karshensa cewa Allah Allah (S.W.T) ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su. “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah sannan ba za a taimake ku”. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul Baiti (AS). Hakika hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.

Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.

Imamai (AS) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba; daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (AS) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai akan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kiraka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”[48].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next