Akidojin Imamiyya



FASALI NA BIYAR

 

43- Tashin Kabari Da Tashin Kiyama

Mun yi imani da cewa Ubangiji zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawarinta, sai ya saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo, wannan al’amari ne da baki dayansa da abin da ya tattara na daga sauki, abu ne wanda dukkan shari’o’in da aka saukar daga sama da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, kuma babu wata madogara ga musulmi sai dai ya yi imani da Akidar Alkur’ani mai girma wacce Annabinmu mai girma ya zo da ita (S.A.W), domin duk wanda ya yi imani da Allah imani yankakke ya kuma yi imani da Muhammad manzo ne daga gare shi wanda ya aiko shi da Shiriya da Addinin gaskiya to babu makawa ya yi imani da abin da Alkur’ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni’ima, da wuta da kuna, kuma Alkur’ani ya bayyana haka a sarari kuma ya yi nuni da shi a cikin abin da ya kai kusan ayoyi dubu.

Idan har shakku ya samu wani game da wannan ba don komai ba ne sai domin yana shakku game da ma’abocin sakon, ko kuma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, ba komai ba ne sai shakkun da yake bujuro masa game da asalin addinai dukkaninsu, da kuma ingancin shari’o’i gaba dayansu.

 

44- Tayar Da Matattu

Tayar da Matattu wani al’amari ne da yake larura daga laruran Addinin Musulunci, Alkur’ani mai girma ya yi ishara game da shi: “Shin mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. A’aha, Lalle mu masu iko akan mu daidaita yatsunsa ne”. Surau Alkiyama: 3. Da fadinsa: “Idan kayi al’ajabi to abin al’ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka mutu muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa”. Ra’ad: 5. Da fadinsa: “Shin mun gajiya ne da halittar farko, a’a su dai suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta”. Surar Kaf: 14.

Tayar da Matattu ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da Matattu fiye da abin da Alkur’ani ya ambata ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi da Siradi da Auna ayyuka da Aljana da Wuta da Sakamako da Ukuba daidai gwarbwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur’ani mai girma.

“Bai wajaba ba sanin hakikar da babu mai iya kaiwa gare ta sai ma’abocin zurfin ilimi, kamar ilimin cewa shin Matattu zasu dawo ne da kan kansu ko wasu makamantansu ne? Kuma shin rayuka zasu rasu ne kamar jiki ko kuwa zasu ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jiki yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanci mutum ne ko ya hada har da dukan dabbobi ne? Kuma shin tashin a lokaci daya ne ko a sannu-sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da Wuta wajibi ne amma bai zama dole a san cewa samammu ne a halin yanzu ba, ko kuma sanin cewa a sama suke ko a kasa ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma’auni ya zama wajibi amma bai wajiba ba a san cewa ma’aunin na ma’ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba dole ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa daidaituwa a kan tafarki madaidaici ne. Hadafi wannan bayani shi ne a Musulunci ba a shardanta bincike domin sanin cewa wadannan abubuwa suna da jiki ne ko kuwa…”[57].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next