Akidojin Imamiyya



7- Siffofin Ubangiji (S.W.T)

Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da irada -nufi-, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.

Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hakikaninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.

Tabbatattun siffofi na idafa[11] kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.

Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa[12] ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa Makadaici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hakikaninsa makadaici sidif.

Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kadaitakar zati da rashin kididdigarsa, amma sai ya fada cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre[13], Allah ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai.

Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, ya yi imani da kididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya[14] gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa madaukakin sarki.

Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:

Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[15], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: Akan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[16].

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next