Akidojin Imamiyya



Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W) da kuma sabanin mazhabobi da ra’ayoyi da samuwar kungiyoyi- ya yi bincike Ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba, jama’a jama’a sun rarraba, babu salla guda daya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri daya ba a cikin dukkan mu’amala... don haka yaya zai yi? ta wace irin hanya zai yi salla? da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da daiyya da sauransu?

Kuma bai halatta gare shi ya bi ra’ayin iyaye ba ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T) domin a nan babu wata alkunya ko sassauci ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar Alkiyama: 36.

“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar AlKiyama: 14.

“Lalle wannan fadakarwa ce ga wanda ya don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.

Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashara masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin Mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu Mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zai ta ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi, har sai ya kai ga wani ga gaskiya a bar dogaro.

Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bincike a kan abin da ke biye da ita a akidar Imamiyya Isna Ashariyya.

 

FASALI NA UKU

 

23- Bayanin Imamanci



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next