Akidojin Imamiyya



Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi[15], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: Akan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin[16].

 

8- Adalcin Allah

Mun yi imani cewa yana daga siffofin Allah madaukaki tabbatattu na kamala cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya take hakki a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hakkin hukunta masu sabo, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta.

Kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau matukar ba wani abin da zai hana aikata shi, kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi mai kudura ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.

Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu ba:

 1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.

2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.

3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.

4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya takaita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next