Akidojin Imamiyya



Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (A.S), mamakin kyawun wannan bayani mai hikima! Mamakin wannan abin nema na ilimi mai zurfi!`                 .

Haka nan ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar Kiyama a cikin kafirai[10] koda kuwa ya kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai, kuma irin masu wannan da’awa sun sandare ne a kan zahirin laffuzan Kur’ani ko hadisai, kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su, suka kuma kasa yin amfani da aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai da ka’idojin aron kalma, da kuma ka’idojin aron ma’anar kalma suke.

 

6- Kadaita Allah (S.W.T)

Mun yi imani cewa ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, kuma mun yi imani da cewa shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarsa, kamar yadda muka yi imani da kadaita shi a siffofi da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan. Mun kuma yi imani da cewa ba shi da kama da shi a siffofinsa, shi a ilimi da kudura ba shi da tamka, a halittawa da arzutawa ba shi da abokin tarayya, a cikin kowace kamala ba shi da kini.

Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.

Amma ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi’a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al’amarin, shi ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa na Addini, da kuma taimakon talaka.

Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa. Haka nan sauran kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda suka hada da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da kai janaza da kuma ziyartar ‘yan’uwa.

Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini suna daga kyawawan ayyuka a shari’a wannan al’amari ne da ya tabbata a fikihu, ba nan ne wajan tabbatar da shi ba. Abin da muke so mu yi bayani a nan shi ne; gudanar da irin wadannan ayyuka ba ya daga cikin irin nau’o’in shirka da Allah kamar yadda wasu suke rayawa, ba kuma bautar imamai ba ne, sai dai abin da ake nufi shi ne raya al’amuransu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next