Akidojin Imamiyya



Dukkan wadannan surori sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.

Sai dai kuma wasu sashen musulmi sun halatta wa Allah (S.W.T) aikata mummuna, suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa yana iya dora wa bayinsa abin da ya fi karfinsu da abin da ba zasu iya ba, tare da haka kuma ya azabtar da su a kan ba su aikata ba. Kuma suka halatta zalunci da danne hakki, da karya da yaudara ga Allah madaukaki, da kuma aikata aikin da babu wata hikima, da manufa, da maslaha, da fa’ida, da hujjar cewa shi: “Ba a tambayar sa a kan abin da yake aikatawa amma su ana tambayar su”. Surar Anbiya: 23.

Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, makaryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa[17].

Kuma Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

“Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23.

“Kuma Allah ba ya son barna”. Surar Bakara: 31

“Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu muna Masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205.

“Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don barna -rashin manufa- ba.

 

9- Hawan Hukunci A Kan Baligi



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next