Akidojin Imamiyya



36- Ziyartar Kaburbura

Ziyarar kaburbura -Annabi da na Imamai (AS)- da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abu mai tsada da mai sauki a cikin imani da dadin rai.

Wannan kuwa asalinsa yana komawa ne zuwa ga wasiyyar Imamai da kuma Zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da yake da shi mai yawa a gurin Allah madaukaki, saboda kasancewarta daga mafifitan ayyuka biyayya da kusanci da Allah bayan ayyukan ibadu wajibai, da kuma cewa kaburburan suna daga cikin mafifitan guraren amsa addu’a da yankewa zuwa ga Allah (S.W.T).

Kuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma yana daga mafificin cika alkawari, ziyartar, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai to zasu kasance masu cetonsu a ranar lahira[40].

Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, hada da sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana kuma cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS) tare da koya musu tsarkin Musulunci da sakonsa da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T) da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauki da sama da haka kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahi” wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S).

Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin imamai (AS) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon na larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa da kowa yake fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin laduban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS) domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) a dunkule, game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya.

Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da samuwar wadannan dabi’u na Addini madaukaka; da ya hada da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa.

Daga nan kuma akwai abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar da kuma bayan ziyarar da mu a nan zamu bujuro da sashen wadannan ladubban domin fadakarwa kan manufarta a muka ambata:

1- Daga ladubbanta, mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa’idar wannan kuwa cikin abin da muka fahimta a fili take, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga dauda domin ya kubutar da shi daga rashin lafiya da cututtuka kuma domin kada mutane su gundara[41] da warinsa ya kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Hakika ya zo a cikin hadisai cewa; mai ziyara ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da wadancan manufofi madaukaka, sai ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da kuma dukkan aibi kuma ka tsarkake zuciyata da gabobina da kasusuwana da namana da jinina, da gashina da fatata, da bargona da kashina da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina.”

2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi a taron jama’a abu ne da mutane suke so wa junansu yake kuma kusantar da su ga junansu tare da kara musu daukaka da jin daukaka a bukin da suke halartarsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next