Akidojin Imamiyya



Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, ko da kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.

Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

 

10- Hukuncin Allah Da Kaddara

Mujabbira[18] sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi akan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa[19], suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika.

Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Ubangiji mahalicci, da ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.

Mufawwada[20] kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.

Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu, al’amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa.

Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al’amari ne tsakanin al’umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce.

Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next