Akidojin Imamiyya



A wani bangaren, Ubangiji madaukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargadi da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi.

Husumar cikin zuciyarsa da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da adifa, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan adifarsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu, wandanda kuwa adifarsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu cibaya a ‘yan Adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi.

Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka”. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kadai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki daya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana kara jahilci ko kuma kara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na dabi’a da sauran samammu na binciken ilimi ya karu ba.

Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana kara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fandarewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi ­da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin wadannan gwagwarmayar dauki-ba-dadi ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi.

Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya kebance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun hadu sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari.

Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargadi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su.

Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa.

Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah madaukakin sarki ya bi shi, Allah ya daukaka ga haka daukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fadinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.

 

15- Mu’ujizar Annabawa



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next