Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Menene Hukuncin Ziyartar Kaburbura?

Ziyarar kaburburan Annabi da na Imamai da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abin da suka mallaka a kan hakan da jin dadin ransu.

Wannan kuwa asalinsa yana komawa ne zuwa ga wasiyyar Imamai da kuma zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da yake da shi mai yawa a gurin Allah madaukaki, saboda kasancewarta daga mafifitan ayyukan biyayya da kusanci da Allah bayan ayyukan ibadu wajibai, da kuma cewa kaburburan suna daga cikin mafifitan guraren amsa addu’a da yankewa zuwa ga Allah (S.W.T).

Kuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma ziyartarsu tana daga mafificin cika alkawari, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai, to zasu kasance masu cetonsa a ranar lahira[21].

Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, akwai sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu, da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna, kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu, da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS), tare da koya musu tsarkin musulunci da sakonsa, da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka, da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T), da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauke da sama da haka, kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahi” wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S).

Wadannan ziyarorin suna fahimtar da matsayin imamai da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya, da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa yake iya fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a, da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin ladubban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS), domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya a dunkule.

Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwa, da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubbanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar, da abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar, da kuma bayan ziyararda wadanda wasu daga cikinsu zuka zo kamar haka:

1- Yin wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, kuma ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da hadafin ziyararsa ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da dukkan aibi, kuma ka tsarkake zuciyata, da gabobina, da kasusuwana, da namana, da jinina, da gashina, da fatata, da bargona, da kashina, da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina”.

2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafinsa.

3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa kamar ta sanya sababbin tufafi ce.

4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next