Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Da an dabbaka Shari’ar Musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da dan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, da kuma zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.

Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko, kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Ba riko da musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa musulmi wannan mummunan cibaya ba, sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu[38].

Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa Aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba. Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasu, babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shudewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima, da camfe-camfe, da surkulle, da kuma yake-yake, da jayayya, da alfahari, sai suka fada a cikin halakar da ba ta da iyaka.

A yau yammacin Turai wayayye, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa[39].

Musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari.

 Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi[40].

Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gagagauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.

Wanene Cikamakon Annabawa?

Cikamakon Annabawa: shi ne ma’abocin sakon Addinin musulunci Annabi Muhammadu dan Abdullahi, shugaban manzanni, mafificinsu, kuma shi ne shugaban halitta baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, ko ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali ko kamarsa a kyawawan dabi’u[41], wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin kiyama[42].

Menene Hakikanin Kur’ani Mai Girma?

Kur’ani wahayin Ubangiji ne, kuma abin saukarwa daga Allah madaukaki a harshen AnnabinSa mai daraja, a cikinsa akwai bayanin komai da komai, shi ne mu’ujiza madawwamiya wadda ta gagari dan Adam ya zo da kamarta a balaga, da fasaha, da azanci, tare da abin da ya kunsa na daga hakika da ilimomi madaukaka, jirkita, ko canji, ko karkacewa, ba sa bujuro masa[43]. Kur’anin da yake hannunmu wanda ake karantawa shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W), duk kuwa wanda ya yi da’awar sabanin wannan to shi mai kage ne, mai kawo rudu, kuma mai rikitarwa, kuma ba a kan shiriya yake ba, domin shi Kur’an zancen Allah ne “Wanda karya ba ta zo masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa”. Surar Fusilat: 42.

Daga cikin dalilan da suke tabbatar da mu’ujizarsa akwai cewa, duk sadda zamani ya cigaba, ilimomi da fannoni suka dada cigaba, Kur’ani yana nan daram a kan danyantakarsa da zakinsa, da daukakar manufofinsa, da abin da ya kunsa na tunani, babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi, kamar yadda ba ya taba kunsar wani warwara game da hakika da yakini na falsafa, sabanin littattafan da malamai da manyan masanan falsafa komai matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani suka rubuta, sai ka samu wani abu na kuskure a cikinsu da tuntube. Kuma Kur’ani yana nan daram duk sadda aka samu cigaba a sababbin bincike na ilimi da sababbin ra’ayoyi. Kurakurai suna bayyana hatta a rubuce-rubucen manyan masana falsafar Yunan kamar su Sakrato, da­ Aplato, da Arasto, da duk wadanda suka zo daga bayansu suka yi musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma fifiko na tunani da amfani da kwakwalwa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next