Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Abin da zai bincika shi ne; Shin ya kama tafarkin Ahlul Bait (A.S) ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashariyya masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarorin daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu Mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zata yi ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi har sai ya kai ga wata gaskiya a bar dogaro.

Menene Hakikanin Imamanci?

Mun yi imani cewa Imamanci yana daga cikin Usuluddin wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi koyi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne, a nemi sani, a yi bincike game da shi, kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.

A takaice, sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa, ya dogara ne a kan imani da imamanci; duk da cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi koyi a cikinsu, amma duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa; sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba sanannu ba ne a yanke, saboda haka wajibi ne mu koma wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, wannan kuwa ba ya samuwa sai ta hanyar imamin da Allah madaukaki ya nada shi ta hannun Annabinsa (S.A.W).

Kamar yadda muka yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam, da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar Duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafiyar da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga cikinsu. A bisa wannan asasin ne imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da yake wajabta aiko da Annabawa da Manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).

Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi[46], ko kuma a bisa harshen imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suke son nadawa, ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a hadisi ingantacce.

A kan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami da yake wajibi a yi masa biyayya ba, wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T), shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakonsa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idanuwan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge, haka nan yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsawo[47].

Menene Hakikanin Ismar Imami (A.S)?

Ismar Imami (A.S) shi ne imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa, kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa, da kuskure, da mantuwa.

Domin imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne a wannan fage, dalilin da ya hukunta mana imani da ismar annabawa kuwa, shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar imami ba tare da wani bambanci ba.

Menene Hakikanin Siffofin Imami?

Siffofin imami kamar yadda siffofin annabi suke ne, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jarumtaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafiyar da al’amura, da hankali, da hikima, da kuma kyawawan dabi’u, dalilinmu na wajabcin samuwar wadannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na wajabcin siffantuwa da wadannan siffofi ga imami.

Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan saninsa ta gurin Annabi ne, ko kuma daga imamin da ya gabace shi. Idan kuwa aka sami wani sabon abu, to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilimi”[48].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next