Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Karfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “Kuwwa kudsiyya” wato karfi ne daga Allah da yake mafi kamalar kololuwar darajar ilhama. Mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami. Sai ya koma wa wannan abin jahiltar domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsaftataccen madubi.

Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu, duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa, kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar ban sani ba daga bakinsu, ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba zaka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruwaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi, kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri.

Menene Nauyin Da Yake Kanmu Game Da Imamai?

Imamai (A.S) su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarki zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar iliminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa, kamar yadda taurari suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W).

A wani hadisin ya zo cewa:    “Misalinsu a wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa, ba sa rigonsa da magana, kuma su da umarninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.

 Kamar yadda yake cewa; Umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba masa ne, kuma soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne. Bai halatta a karbi hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu.

Karbar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma mujtahidan da ba sa biyayya ga tafarkinsu kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu, nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya, wacce ya hakikance cewa da ita ce zai isa zuwa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajabcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.

Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tafki”[49].

Kamar yadda wasu hadisai suka siffanta su da; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya bar su, to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba, gudu ne daga gaskiya da ba abin da yake kaiwa ga hakan sai son rai da ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici[50].

Menene Hakikanin Son Ahlul Baiti (A.S)?

Son Ahlul Baiti (A.S) yana daga mafi girman wajibi da Allah (S.W.T) ya dora wa bayi gaba daya, ya kuma sanya wannan son shi ne abin da al’umma zata saka wa manzo (S.A.W) da shi[51] na godiya gareshi sakamakon shiryar da ita da ya yi, kuma hadisai sun zo ta hanyoyi masu yawa cewa; Son su alamar imani ne, kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da manzonsa, wanda kuma ya ki su to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).

Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasib” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyar Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin munafunci son su kuma ya zama daga alamomin imani, kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da Manzonsa (S.A.W).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next