Tambayoyi Da Amsoshin Akida



3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.

4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya takaita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.

Dukkan wadannan surori sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna[14].

Ayoyi da yawa sun tabbatar da hakan a cikin kur'ani mai girma, kamar fadinsa: “Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23. “Kuma Allah ba ya son barna”. Surar Bakara: 31. “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu muna Masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56.

Mecece Kaddarawar Allah Madaukaki?

Kaddarawar Allah ga al'amura ba ya nufin ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu, kuma ba ya nufin ya bar bayi sakaka ba tare da yana da iko a kansu ba, al'amarin kamar yadda ya zo daga imamai masu tsarki yana tsakanin wadannan al'amura biyu ne, al’amarin da wasu masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa.

Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu”.

Abin nufi shi ne; ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne masu aikata su, kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah da mulkinsa ne, domin Shi ne mai bayar da samuwa, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al’amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa.

Al’amarin imani da kaddara ya wadatar mutum ya yi imani da shi a dunkule yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al’amari ne tsakanin al’amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka.

Masu ra'ayin cewa kaddarawar Allah ga al'amura tana nufin ya tilasta bayi ne[15] sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi a kan cewa ayyukansu tabbas ayyukansa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa[16], suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika, wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.

Masu ra'ayin cewa Allah ya saki bayi ba tare da yana da wani iko da kaddarawa ko juya al'amuransu ba[17] sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinsa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa[18].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next