Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Mecece Takiyya?

Takiyya tana da tushe mai karfi daga Kur'ani mai girma da hadisai madaukaka kamar haka; An ruwaito daga Imam Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya Addinina ce kuma Addinin iyayena ce”. Da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi”.

Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu, da kare jininsu, da kawo gyara ga halin da musulmi suke ciki, da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi’a da ita tsakanin sauran bangarori na al’ummu, kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi, ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye, ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar hankali take hukunci da shi.

Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwadon sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama halal, ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addini, da hidima ga musulunci, da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce, kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kaiwa ga kashe rayuka masu alfarma, ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su, ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu.

Wadanda suke son aibata shi’a sun samu damar amfani da akidarmu ta takiyya, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai ba sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba, da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata, da ya isa a ce wannan dan shi’a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa, da Abbasawa, da kuma Usmaniyawa. Idan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar’ancinsa a addini, to mu sai mu ce masa:

Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga Addini a wajensu, kuma ka ji fadin Imam Sadik (A.S) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi.”

Na biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Kur’ani mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imani”. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya”. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye imaninsa Ya ce”. Surar Gafir: 28.

Menene hakikanin ma’anar Annabci?

Annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji madaukaki da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan’adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta daukaka zuwa ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da lahira.

Ka’idar tausasawa ta wajabta ga Allah mahalicci mai ludufi ga bayinsa, da ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinsa. Kuma Allah madaukaki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba, ko tsayar da shi takara, ko zabensa ba. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonsa”. Surar An’am Aya ta 124.

Kamar yadda mutane ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a.

Menene Hakikanin Sirrin Annabci?

Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da dabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane daya daga cikin mutane, dabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda dabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa[30], ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan dabi’u[31] daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwadayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta[32], da sauran dabi’un halitta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next