Tambayoyi Da Amsoshin Akida



[34] - “Manzanni masu bushara kuma masu gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan Manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Nisa’i: 165.

[35] - Duba fadin Allah madaukaki “Kuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan Kur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe”. Surar Isra’i: 88.

“Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Hud: 13.

kalubalantar su kan su kawo sura daya kamarsa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura daya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23. Ubangiji madaukaki yana cewa:---

 --- “Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda daya kamarsa kuma ku kira duk wanda zaku iya koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.

[36] - Akidojin imamiyya, babin mu’ujiza

[37] - Isma ita ce rashin aikata sabo a kowane hali na zamani a rayuwa, shin a lokacin yarinta ne ko girma ko tsufa, kafin aike da lokacin aike.

[38] - “Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu ”. Surar Anfal 53. Da: â€œKuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17. Da fadinsa Madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.

Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.

[39] - Allah Madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next