Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da Manzonsa, da tsarkinsu, da nisantar su ga shirka da sabo, da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa; Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa, domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba, da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.

Menene Muka Kudurce Game Da Imamai (A.S)?

Mu muna kudurcewa da cewa; Imamanmu mutane ne kamar mu, suna da abin da yake garemu, kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa, Allah ya kebance su da karamarsa, kuma ya so su da soyayyarsa, domin suna da karamarsa, kuma ya ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumtaka, da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita, da siffofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.

Da wannan ne suka cancanci su zamo Imamai masu shiryarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa, da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.

Imaminmu Ja’afar Sadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi, ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada kuyi musun sa, ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.

Menene Hakikanin Maganar Nassi A Kan Imamanci?

lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa, ko harshen imamin da aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da imamin bayansa, hukuncin imamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani banbanci ba. Mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya, da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya, wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.

Hakika Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Dalib Amiri ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama, kuma ya nada shi, kuma ya karba masa bai’a a kan shugabancin Muminai Ranar Gadir Yana mai cewa: “A saurara a ji! Duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa ne, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, kuma ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya”.

Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancinsa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana, kuma wasiyyina, kuma halifana a bayana, ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuwa shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa da yawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne, sai dai babu Annabi a bayana”. Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar:

“Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u”. Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u.

Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS), haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo.

Nawa Ne Adadin Imamai?

Imaman da suke da siffar jagoranci na gaskiya, wadanda suke makomarmu a cikin hukunce-hukuncen shari’a, wadanda Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da su da sunayensu gaba daya, sannan wanda yake gabata yana wasiyya da mai biye masa sun kasance kamar yadda yake a wannan jeri ne da da alkunyarsu da lakabinsu da tarihin haihuwarsu da rasuwarsu;



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next