Tambayoyi Da Amsoshin Akida



[8] - Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alaka tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.

[9] - Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.

[10] - Wasu daga Mu’utazilawa sun tafi a kan cewa Allah ba a siffanta shi da siffofi tabbatattu domin gudun kada a kamanta shi da bayinsa; wato ba a siffanta shi da ilimi ko iko, sai dai a kore masa jahilci da gajiyawa. Abin da suka kasa fahimta a nan shi ne sun kore wa Allah dukkan kamala da wannan magana tasu, domin shi mai kamala maras iyaka, amma halittu a kamalarsu suna da iyaka.

[11]- Wannan ra’ayi ne na Ash’ariyya da suke ganin siffofin ma’ani ba kawai ma’ana ba ne da Allah shi ne hakikanisnsu na zahiri, kamar yadda sauran siffofinsa suke, sai dai wadannan siffofi suna da tabbatattun hakikaninsu a zahiri na hakika da suke siffantuwa da su. Wato kamar Ali da yake da sunaye ne da siffofi, da za a ce masa Ali, dan Muhammad, baban Isa, dogo ne, kuma kakkaura da sauransu, sai a ce siffofinsa dan Muhammad, baban Isa, da dogo, da kakkaura, duk a zahiri suna da daidaikun da suke siffantuwa da su, sai ya zama Ali shi yana nuni izuwa gareshi ne kawai banda sauran siffofi, sauran siffofi kuma suna da nasu hakika da suke siffantuwa da su a zahiri. Da maganar Ash’ariyya gaskiya ne da a nan Allah ya zama guda takwas, kamar yadda a misalinmu Ali zai zama su biyar, wato Ali, da dan Muhammad, da baban Isa, da dogo, da kuma kakkaura.

[12] - Wato siffofn kari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dadu ga zatin Allah kuma zatin yana bukatarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu.

Na biyu; Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah da idonsa da fuskarsa da suke da tawili da ma’anar da larabawa suka sani a lokacin saukar da littafin Kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin- --hannu da karfi, ko iko, ko alkawarin Allah, kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a Kur’ani mai girma.

[13] - Alhalin Allah yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba.

 

[14] - Akidojin Imamiyya, Babin adalci da kuma kallafawa bayi ayyuka.

[15] - Su ne mutanen da suka tafi a kan cewa ayyukan bayi a bisa hakika ayyukan Allah ne ba tare da wani tawili ba a kan haka, don haka Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan bayi kai tsaye.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next