Tambayoyi Da Amsoshin Akida



[40]- Fadinsa madaukaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuma sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo rahama da imamai cewa ; Mahadi daga ‘ya’yan Fadima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.

[41]- “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Kalam 4.

[42] - Amirul muminin Aliyyu Dan Abi Dalib (A.S) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa, ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).

[43]- Ubangiji madaukaki yana cewa: “Mu mu ne muka saukar da ambato kuma lallai mu masu karewa ne gare shi”. Surar Hijri: 9.

[44]- Duba fadinsa madaukaki: “Kuma yayin da Isa dan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.

[45]- “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar kiyama: 36. “Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar kiyama: 14. “Lalle wannan fadakarwa ce, don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.

[46]- Madaukaki ya ce: “Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8. Da kuma fadinsa: “Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fadir: 22.

[47]- Fadinsa madaukaki: “Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah ya riga ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma’abucinsa kada ka damu hakika Allah yana tare da mu, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa gareshi ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Tauba: 40.

[48] - Kamar yadda yake a fadar Ubangiji “Ka ce Ya Ubangiji! Ka kara mini ilimi”. Surar Taha: 114.

[49] - Masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun hadu a kansa.

[50] - Littafin Akidojin imamiyya, babin imamanci.

[51] - Ubangiji ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23.

[52] - Akidojin Imamiyya, imaninmu game da imam Mahdi.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29