Tambayoyi Da Amsoshin Akida



 Friday: 10 Ramadan 1426

14 October 2005

22 Mihir 1384


Shin Ya Halatta A Yi Koyi Da Wani A Usuluddin?

Ba ya inganta ba a yi koyi da wani a cikin shika-shikan addini da aka san su da Usuluddin, don haka abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yancin hankali. Don haka ya wajaba a kan mutum mai hankali ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari a kan asasin shika-shikan akidarsa wadanda suka hada da :

1.      Kadaita Allah

2.      Annabci

3.      Imamanci

4.      Tashin kiyama

Duk wanda ya yi koyi da iyayensa ko kuma wasunsu a imani da wadannan shika-shikan to lalle ya kauce wa tafarki madaidaici, kuma ba zai taba zama abin yi wa uzuri ba har abada[2].

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next