Tambayoyi Da Amsoshin Akida



Menene Muka Sani Game Da Bada?

Bada shi ne wani sabon ra’ayi da ya bayyana ga mutum wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra’ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata.

“Bada” da wannan ma’anar mustahili ne ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa, wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi’a Imamiyya ba su yarda da shi ba. Imam Sadik (A.S) ya ce: “Wanda ya yi da’awar cewa canji cikin wani abu ya faru ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama, to a gurinmu wannan ya kafirta da Allah mai girma”. Kuma ya ce: “Wanda ya raya cewa wani abu na canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda ya kasance bai san shi ba jiya to ka barranta daga gareshi”.

Muna iya bayar da misali da hadisi daga imam Sadik game da Bada da yake cewa: “Wani abu bai taba bayyana ba ga Allah kamar yadda ya bayyana gareshi game da Isma’ila dana”. Har wadansu daga marubutan musulmi suka danganta Bada ga Shi’a Imamiyya da waccan ma’ana domin suka ga mazhaba kuma tafarki na Ahlul Baiti (AS), suka sanya wannan daya daga abubuwan da suke suka da aibata shi’a da shi. Ubangiji madaukaki yana fada a littafinsa ne cewa: “Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take ”. Surar Ra’ad: 39.

Ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) a nan ita ce: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.

Bada a nan yana nufin Allah (S.W.T) yana iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki.

Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada” shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su[19].

Mecece Raja’a (Komowa Duniya)?

Raj'a tana nufin cewa; Allah madaukaki zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma saka wa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).

Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna, sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashin kiyama, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuma azaba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Kur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu, to mun yi furuci da zunubanmu, shin akwai wata mafita”. Surar Mumin: 11.

Kur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya, kuma hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, haka nan mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa, ma’anarta ita ce komowar hukuma da umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S), da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko rayar da matattu.


Imani da Raja’a yana kara inganta imani, domin ita dalili ce a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa, kuma ita tamkar mu’ujizar rayar da matattu ce da ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma, domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next