Tambayoyi Da Amsoshin Akida



11 Abu Muhammad Hasan Askari Shekara 232 H zuwa 260H

12 Abul Kasim Muhammad Mahdi       Shekara 256H zuwa .....

Imam Mahadi (AS) shi ne hujjar allah a zamaninmu kuma boyayyen da ake sauraro, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukaka mafitarsa, zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cike ta da zalunci.

Mecece Hakikanin Magana Game Da Mahadi (A.S)?

Hadisai sun tabbatar da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) a karshen zamani, wanda zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci, kuma wannan ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa, kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun rawaito hadisai game da shi.

Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda izasu da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci, kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba, ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar Kaisaniyya, da Abbasawa, da wasu daga Alawiyyawa, da sauransu, ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a.

Kasancewar musulunci shi ne addinan Ubangiji na karshe, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya, ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashe duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen musulmi, da kuma rashin lizimtuwarsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi.

Sannan kuma ba zai yiwu ba musulunci ya dawo da karfinsa da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya ba, alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau na sabanin mabiyansa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa, da bata a cikin da’awoyinsu.

Ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata, tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya, da kuma iko da ya wuce na al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.

Sai dai kawai bambancin da ke tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne; ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekarar hijira ta 256, kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad”, wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi da imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa, da haihuwarsa, da boyuwarsa.

Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari, wanda kuwa wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next