Tambayoyi Da Amsoshin Akida



A wani bangaren, Ubangiji madaukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargadi da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi.

Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kadai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki daya da kuma al’ummar da take kewaye da shi.

Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya.

Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da annabawa da manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su[33]. Domin su yi wa mutane gargadi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, a gare su.

Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarsa, shi mai tausasawa ne ga bayinsa, mai yawan baiwa, mai karimci, ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah madaukaki ya bi shi, Allah ya daukaka ga haka daukaka mai girma! ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fadinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.

 

Menene Hakikanin Mu’ujizar Annabawa?

Mu’ujiza wani dalili ne da Ubangiji ya kan sanya shi ga mutane domin ya sanar da su gaskiyar annabawansa daga gareshi, da kafa musu hujja domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu[34], kuma ya zama ya gagari kudurar dan Adam.

Yakan sanya wannan karfi da iko a hannun annabi ta yadda duk sa’adda bukatar hakan ta taso sai ya aiwatar da shi ga mutane da izinin Allah domin a san gaskiyar manzancinsa da shi. Wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa.

Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa.

Idan irin wadancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon dan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar dan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum kuma ya yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa.

Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da daukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya dimautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu[35].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next