Tambayoyi Da Amsoshin Akida



5- Ya tafi yana mai nutsuwa da kwanciyar hankali, mai runtse ganin idonsa daga haram.

6- Ya yi kabbara da fadin: “Allahu Akbar” ya yi ta yadda ya so, kuma a wasu ziyarorin an kayyade kabbarorin zuwa dari.

7- Bayan kammala ziyarar ga Annabi ko ga Imami sai ya yi salla mafi karanci raka’a biyu domin bauta ga Allah da godiya gareshi saboda dacen da ya yi masa, ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. Bayan salla sai ya karanta wannan addu’a: “Ya Uabangiji gareka na yi salla, gare ka na yi ruku’u, gareka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin salla da ruku’u da sujada ba sa kasancewa sai gareka, domin kai hakika kai ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Uabangiji ka yi tsira da aminci ga Muhammad da Zuriyar Muhammad kuma ka karbi ziyarata, ka ba ni abin da na roka, domin Muhammad da Zuriyarsa masu tsarki”.

8- Ya lizimci kyautata abotakar wanda yake tare da shi, da karanta magana sai dai da alheri, da yawaita ambaton Allah, da kaskan da kai, da yawaita salla, da salati, da runtse idanuwansa, kuma ya taimaka wa mabukata daga cikin yan’uwansa idan ya ga guzirinsu sun yanke, da taimaka musu, da tsantseni kan abin da aka hana, da nisantar husuma ko yawaita rantsuwa da jayayya[22].

Ba komai ne hakikanin ziyara ba sai salati ga Annabi da Alayensa (A.S), da la’akarin cewa “Su rayayyu ne ana arzuta su gun Ubangijinsu”, kuma suna jin magana suna amsawa, kuma ya isa ya ce: Assalamu alaika ya RasulalLah! Sai dai abin da ya fi, ya karanta abin da aka rawaito na hadisai da suka zo game da ziyara daga Ahlul Baiti (A.S), saboda abin da yake cikinta na daga manufofi madaukaka da fa’idoji na addini, tare da balagarta da fasaharta, da kuma abin da yake cikinta na daga addu’o’i madaukaka da mutum yake fuskanta zuwa ga Allah makadaici a cikinta[23].

 

Menene Hakikanin Shi’anci?

Ahlul Baiti (AS) ba su da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga garesu, don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su, kuma suka aminta da shi a kan sirrinsu, suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa, da kuma wanda yake kansa.

Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu ne kuma shi’arsu sai idan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa, mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin sha’awarsu da son ransu wadanda ke neman hanyar fandare wa bin Allah, Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana, da tsentseni da tsoron Allah.

“Ya Khaisama! Ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar kiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa”[24].

Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku”[25].

A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 next