Akidojin Imamiyya



 

13- Bayanin Annabci

Mun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji (S.W.T) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta daukaka zuwa ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da lahira.

Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai ludufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah madaukakin sarki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zabensa. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa”. Surar An’am Aya ta 124.

Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a.

 

14- Annabci Tausasawa Ne

Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da dabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane daya daga cikin mutane, dabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda dabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa[21], ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan adifa[22] da dabi’o’i daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwadayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta, da tarkacenta, kamar yadda Madaukakin sarki yake cewa:

“Hakika mutum yana cikin hasara”. Surar Asri: 2. “Hakika mutum yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata”. Surar Kalam:6-7.

“Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake kunshe da adifa da kuma sha’awa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next