Akidojin ImamiyyaFASALI NA HUDU Tarbiyyar Ahlul Bait Shimfida: Ahlul Baiti (AS) sun sani tun tuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa. Don haka a bisa dabi’a suka riki “takiyya†a Addini da dabi’a garesu da su da mabiyansu matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ba ko Addini, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS). Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar Musulunci da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani domin su zama misalai na musulmi na gari mai adalci. Tafarkin Ahlul Baiti (A.S) wannan dan littafi ba zai iya kawo dukkansu ba, akwai littattafan hadisai masu girma da suka dauki nauyin yada ilimin addini, sai dai ba laifi mu yi nuni da wasu da suke kama da babin akida cikin abin da ya shafi tarbiyyantarwarsu ga shi’arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al’amuran zamantakewar al’umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki suke kuma tsarkake zukatansu daga dauda zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. Kuma magana ta gabata a game da takiyya da take daya daga tarbiyyar mai amfani ta zamantakewarsu, kuma zamu ambaci sashen abin da ya shafe mu na wadannan ladubban a nan.
|