Akidojin ImamiyyaSahihiyar magana a nan ita ce, mu muna fadi kamar yadda ubangiji ya fada a littafinsa ne cewa: “Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take â€. Surar Ra’ad: 39. Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki. A nan sai ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) ta zama cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa. Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada†shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su. 12- Hukunce-hukuncen Addini Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu. Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali. Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka -sabo- mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (T.A.U.K). A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukakin sarki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.
|