Akidojin Imamiyya[21] - “Da rai da abin da Ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma takawartaâ€. Surar Shamsi: 7-8. [22] - Adifa al’amura ne kamar ki, so, fushi, yarda, da sauran halayen rai da zuciya. [23] - “Manzanni masu bushara kuma masu gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan Manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikimaâ€. Surar Nisa’i: 165. [24] - “Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana hadiddiye abubuwan da suke kirkira. Kuma gaskiya ta tabbata abin da suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka rinjaye su a nan sa’annan suka juya suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna masu sujadaâ€. Surar A’araf; 117-120. [25] - “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abin da yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa sai ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya matattu da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abin da kuke ci da wanda kuke taskacewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminaiâ€. Surar AI- Imran: 49. [26] - Duba fadin Allah madaukakin sarik: “Kuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan Alkur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sasheâ€. Surar Isra’i: 88. “Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiyaâ€. Surar Hud: 13 kalubalantar su kan su kawo sura guda kamarsa: “Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura daya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiyaâ€. Surar Bakara: 23
|